Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton ta yi nasara a zaben share fagen tsaida dan takarar shugaban kasa a bangaren jam’iyyar Democrat


‘Yar majalisar dattajai mai wakiltar New York, Hillary Clinton ta yi nasara a zaben share fagen tsaida dan takarar shugaban kasa a bangaren jam’iyyar Democrat, wanda aka yi a New Hamphshire, a yayin da dan majalisar dattabai mai wakiltar Arizona John McCain ya yi nasara a bangaren jam’iyyar Republican.

A cikin jawabin ta na nuna murnar nasarar da ta yi, ’yar majalisar dattajan mai wakiltar New York kuma uwargidan tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ta ce a shirye ta ke ta bama Amurka irin nasarar da New Hampshire ta ba ta.

Obama wanda ya zi na biyu, kud da kud ya taya Hillary murna sannan kuma ya ce yakin neman zaben da ya ke yi zai ci gaba da wakiltar miliyoyin muryoyin mutanen da ke neman canji.

XS
SM
MD
LG