Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Jam’iyyar Hamayya a kasar Kenya tace zata ci gaba da zanga zanga


Babbar Jam’iyyar Hamayya a kasar Kenya tace zata ci gaba da zanga zangar nuna rashin amincewa da da sake zaben shugaban kasar, Mwai Kibaki. Jam’iyyar ODM ko Orange Democratic Movement a turance,tana kira ga magoya bayanta su halarci gangami da za;ayi ranar laraba mai zuwa a dandali Uhuru dake Nairobi.

A sanarwar da babban sakataren Jam’iyyar na kasa Anyang Nyongo, ya bayar a yau Jumma’a ya bukaci ‘Yan sanda su samara da tsaro. ODM tayi kokarin hada irin wannan gangami cikin makon jiya amma ‘Yan sanda suka hanasu,sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa wajen tarwatsa su.

Kokarin da TA tayi na shiga tsakani har zuwa jiya Alhamis yaci tura. Shugaban TA John Kufor na Ghana, ya bar Nairobi ba tareda samun nasara cimma yarjejeniyar ko samun ayi zaman shawarwari tsakanin shugaba Mwai Kibaki, da Raila Odinga na ‘yan adawa ba. Tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan zai karbi kokarin shiga tsakani.

XS
SM
MD
LG