Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush ya isa Saudiyya


Shugaba Bush ya isa Saudiyya, inda ake sa ran zai nemi goyon baya ga shirin wanzarda zaman lafiya tsakanin Israila da falasidnu, da kuma kokarin shawo kan Iran.Mr Bush yana amfani da rangadin da yake yi a gabas ta tsakiya, wajen neman kasashen Larabawa kawayen Amurka, su tallafawa Shugabannnin Falasdinu da kudi da kuma difilomasiyya a shawarwari da sukeyi da Isra’ila.

A jawabinsa jiya lahadi a Abu Dhabi,shugaban ya bukaci kasashe dake yankin tekun Pasha, da su hada kai da Washington wajen tinkarar abinda ya kira, “kasa da ta fi ko wacce a Duniya tallafawa ta’addanci”. Kasashen da al’umar su ‘yan ahlil sunni ne dake gabar tekun Pasha suna ci gaba da hulda da Iran,duk da damuwarsu kan bunkasar ikon Farisar a yankin.

Haka kuma ana sa ran tattaunawar da Mr.Bush zaiyi da shugabannin Saudiyya zai hada harda batun cinikin makamai. Kamin ya tashi zuwa Saudiyya, Shugaba Bush ya kai wata yar gajeruwar ziyara Dubai. Ya gayawa wani taron matasa shugabannin Larabawa cewa, Amurka tana mutunta addininsu,kuma tana so tayi aiki tare dasu cikin lumana. Domin ma karrama ziyarar shugaba Bush zuwa Dubai,gwamnatin Dubai ta bada yau hutu,kuma ta rufe manyan hanyoyi da gadoji domin tsaro.

Mr.Bush ya soma rangadin birnin, da kai ziyara gidan tsohon sarkin Dubai, Sheikh Saeed Al Maktoum,wadda aka maidashi wurin adana kayan tarihi cike da hotuna da kayan gargajiyar kasar da suka shude. Daga bisani Mr.Bush yayi zaman cin abincin rana da dalibai dake nazarin Mulki a Makarantar Dubai dake horaswa kan makaman Mulki. Dubai ce kasa ta biyu cikin daular kasashen Laraba, da Mr.Bush ya yada zango. Tunda farko a yau,ya ziyarci wani baje koli kan makamashin zamani a fadar kasar, Abu Dhabi.

XS
SM
MD
LG