Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akasarin kasuwannin shunkun kasashen Asiya a yau sun dan farfado


Akasarin kasuwannin shunkun kasashen Asiya a yau sun dan farfado, kazalika, farashin hannayen jari a kasuwannin turai sun fara nunfasawa sama bayan hucin da kasuwannin hannayen jarin Amurka suka fara a daren jiya.

A hantsin larabar jiya ce kasuwannin jarin Amurka suka fara tafiyar wahainiya, amma kwatsam dab da faduwar rana sai alkaluman hannayen jarin suka yi sama. Kwaramniyar da hannayen jarin kasuwannin Amurka suka sha a farkon makon nan ya sanya zazzabi a kasuwannin hannayen jarukan duniya, amma sai Baitul malin Amurka yayi wufa ya rage uku bisa hudun kudin ruwa daga cikin kashi dari.

kazalika Gwamnatin shugaba Bush da ’yan majalisar dokokin Amurka sun hada karfi domin farfado da karfin aljihun masu sayayya.

XS
SM
MD
LG