Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kibaki ya ga na da babban shugaban hamayya a karo na farko tun kammala zabe 


Shugaban Kenya ya ga na da babban shugaban hamayya a karo na farko tun kammala zabe mai takaddama, da ya jawo tashe tashen hankula har ya kai hasarar rayuka a kasar ta Kenya dake gabashin Afirka.

Shugaba Mwai Kibaki, ya gana da shugaban ‘yan hamayya Raila Odinga, na kusan sa’a daya a yau Alhamis, a tsakiyar fadar kasar Nairobi tareda toshon sakataren MDD Kofi Annan. Bayan ganawar ce,Kofi Anan, yace yana ganin abokanan hamayyar sun dauki matakin farko wajen warware rikicin cikin lumana.

Mr. Odinga yace zaiyi bakin kokarin sa na warware wannan rikici,shi kuma a nasa bangaren, Mr. Kibaki yace shi da kansa zaiyiwa Kenya jagorancin hada kan kasa da zaman lafiya.

Shugabannin biyu duka sun kirayi ‘yan kasar Kenyan su kauracewa tashe tashen hankula. Fadace fadacen kabilanci,da arangama tsakanin ‘Yansanda masu zanga zanga sunyi sanadiyyar mutuwar mutum dari bakwai a Kenya tun zaben na ranar 27 ga watan Disemba. ‘Yan hamayya suna sukar shugaba Mwai Kibaki, da magudin zabe domin tabbatar da dorewarsa kan mulki.

XS
SM
MD
LG