Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata John McCain Ya Lashe zaben Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Republican A Florida


Sanata John McCain daga Jihar Arizona ya doke tsohon gwamnan Jihar Massachusetts, Mitt Romney, a zaben neman tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican a Jihar Florida.

Nasarar da McCain ya samu jiya talata ta jaddada matsayinsa na dan takarar dake kan gaba a cikin masu neman jam’iyyar Republican ta tsayar da su takarar shugaban kasa kafin manyan zabubbukan tsayar da dan takarar da za a yi ranar talata mai zuwa a jihohi fiye da ashirin.

A bayan da aka kidaya fiye da kashi casa’in cikin dari na kuri’un da aka kada, McCain yana da kashi 36 cikin dari, yayin da Romney yake da kashi 31 cikin dari. Ma’ana dukkan wakilan Jihar Florida su hamsin da bakwai sun zamo na John McCain a lokacin babban taron tabbatar da dan takara.

A cikin jawabin godiyar nasara, McCain ya godewa abokan hamayyarsa ya kuma ce akwai sauran aiki a gaba. McCain ya ce, "a cikin mako guda, zamu gudanar da zabubbukan tsayar da dan takara wadanda suka fi kowanne kama da na kasa baki daya. Ina da niyyar lashe zabubbukan tare da zamowa dan takarar shugaban kasa na wannan jam’iyyar."

Kafofin labarai sun ce tsohon magajin garin New York, Rudy Giuliani, wanda ya zo na uku a bayan da ya tara dukkan kwadayinsa a kan lashe Jihar Florida, zai janye daga wannan takara a yau laraba, zai kuma yi mubaya’a ga John McCain.

Shi kuwa Mitt Romney ya fadawa magoya bayansa a wani gangami cewa har yanzu fa wannan gwagwarmaya ba ta kare ba, kuma zai ci gaba da yakin neman zabensa a kan bukatar kawo sabbin ra’ayoyi da dabaru a Washington. Tsohon gwamnan na Jihar Massachusetts ya ce, "turba mafi a’ala ga Amurka ita ce ta karfafa jama’arta, ba wai karfafa gwamnatinmu ba. Idan muna son yin haka, dole ne mu canja Washington, kuma wannan sauyin zai fara ne daga gare mu."

A bangaren ’yan Democrat kuwa, sanata Hillary Clinton ta New York ita ce ta lashe zaben jam’iyyarta ta doke sanata Barack Obama. Sai dai kuma wannan nasara da ta yi ba ta da wata ma’ana, a saboda tun farko uwar jam’iyyar Democrat ta kasa ta kwace wakilan Jihar Florida a saboda reshen jihar ya sauya ranar gudanar da zabensa ba tare da izni ba.

XS
SM
MD
LG