Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Bai Ji Dadin Ganin Afirka Ta Kudu Ta Kasa Warware Rikicin Siyasar Zimbabwe Ba


Shugaba Bush ya ce bai ji dadin yadda shiga tsakanin da Afirka ta Kudu take yi ya kasa warware sabanin siyasa a kasar Zimbabwe ba.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida kafin ya kai rangadi zuwa kasashen Afirka, Mr. Bush ya ce ya dauka gwamnatin Afirka ta Kudu zata rungumi manufar kashe wuta tun kafin tasowarta a kokarin taimakawa al'ummar kasar Zimbabwe.

Har ila yau, Mr. Bush yayi tur da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe a matsayin dan mulkin kama-karya wanda ya rasa mutuncinsa, ya kuma nakkasa kasarsa.

Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu yana shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin Mr. Mugabe da 'yan hamayyar kasar Zimbabwe. A duk tsawon wannan shiga tsakanin, Mr. Mbeki ya ki yarda ya fito da kakkausar harshe yana sukar Mr. Mugabe, wanda zai nemi kujerar shugabancin Zimbabwe a karo na shida a watan Maris.

A yau jumma'a aka shirya shugaba Bush zai tashi don rangadin kasashe biyar a nahiyar Afirka. Mr. Bush zai ziyarci kasashen Benin, Tanzaniya, Rwanda, Ghana da kuma Liberiya. Sai dai kuma shugaban na Amurka ya fada jiya alhamis cewa yana iya jinkirta tashinsa idan har hakan zai taimakawa majalisar wakilan tarayya wajen zartas da sabbin dokokin leken asiri a cikin gida wadanda gobe asabar wa'adin aikinsu zai cika.

XS
SM
MD
LG