Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsinci Konanniyar Gawa A Ofishin Jakadancin Amurka A Belgrade


An tsinci konanniyar gawar wani mutum a cikin ofishin jakadancin Amurka dake Belgrade, a bayan da Sabiyawa ’yan zanga-zanga suka cunna wuta a ginin don bayyana rashin jin dadin goyon bayan da Amurka ta bayar ga ayyana ’yancin Kosovo.

Wani kakakin ofishin jakadancin ya ce da alamun gawar ta wani dan zanga-zanga ne wanda wuta ta rutsa da shi. Jami’an ofishin suka ce babu wani ma’aikaci ko guda da ba a san inda yake ba.

'Yan zanga-zangar sun balle daga cikin wasu masu yin zanga-zangar lumana a birnin Belgrade, suka kai farmaki a kan ofishin jakadancin jiya alhamis, suka cunna wuta a waje da kuma cikin wani ofis.

A bayan mutum guda da ya mutu, mutane fiye da casa'in suka ji rauni a arangama da 'yan sandan Serbia dake kokarin kashe wutar wannan tarzoma.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana kai farmaki kan ofishin jakadancin nata a zaman abinda ba za a amince da shi ba, ta kuma ce Serbia ba ta bayar da tsaron da ya kamata ba. Kakakin ma'aikatar, Sean McCormack ya ce hukumomin Serbia sun tura wadatattun 'yan sanda ne kawai a bayan da aka shiga cikin ofishin jakadancin.

XS
SM
MD
LG