Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kotun musamman a Najeriya ta tabbatar da zaben shugaba Umaru Musa ’Yar Adua da


Talatar nan, kotun ta sauraren karar zaben shugaban kasa ta yanke cewa kalubalantar zaben da ’yan takarar jam’iyyun hamayya Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar su ka yi, ta kasa nuna shaidar abubuwan rashin gaskiyar da su ka yi yawan da ya isa ya soke sakamakon zaben.

Wata kotun musamman a Najeriya ta tabbatar da zaben shugaba Umaru Musa ’Yar Adua da aka yi cikin watan afrilun shekarar dubu biyu da bakwai. Atiku Abubakar ya fada jiya litinin cikin wata sanarwa cewa idan alkalai su ka ce zaben ingantacce ne, zai yarda da sakamakon.

Ya yi kira ga magoya bayan shi su zauna lafiya cikin kwanciyar hankali koma wane irin hukunci aka yanke.

A watan afrilun da ya gabata, an ce shugaba ‘Yar Adua ya yi gagarumar nasara a zaben da ’yan kallon kasashen duniya daban-daban su ka ce, ya na cike da kura-kuran da su ka kawo cikas. Har yanzu masu kalubalantar zaben shugaban kasar na da sauran damar kaukaka karar su a kotun koli.

XS
SM
MD
LG