Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin amurka ta harba harsashe mai linzami a kudancin Somalia yau da asuba


Rundunar sojin amurka ta harba harsashe mai linzami a kudancin Somalia yau da asuba a yunkurinta na kashe wani da ake kyautata zaton memban kungiyar al-qaida ne.

kakakin ma’aikatar tsaron amurka Bryan Whitman ya shaidawa manema labarai cewa an kai harin ne kan wani da aka san fitaccen dan ta’adda ne memban kungiyar al-Qaida. Whiteman bai kara haske game da harin ba.

Sai dai shaidu sun ce a kalla harsasai masu linzami guda biyu ne suka ragargaza wani gida a Dobley kusa da kan iyakar Kenya. Mazauna wurin sun ce harin ya jikkata mutane da dama.

Akwai sabanin rahotanni kan ko harin ya yi sanadin rasa rai. Mazauna Dobley sun ce wani babban malamin islama, Hassan Turki yana garin jiya lahadi domin ganawa da wasu mayaƙan sa kai. Wannan ne karo na uku daga farkon shekarar da ta gabata da Dakarun amurka suka kai hari wuraren da suke kyautata zaton matsugunan ’yan ta’adda ne.

XS
SM
MD
LG