Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Iraqi sunce 'yar harin kunar bakin wake ta tarwatsa kanta aHukumomin Iraqi sunce 'yar harin kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a


Hukumomin Iraqi sunce 'yar harin kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a kofar gidan wani Basarake a lardin Diyala,ta kasheshi da wasu mutane uku. 'Yan sanda suka ce 'yar harin ta tada nakiyoyin da tayi sulke dasu yayin da Sheikh Ghadban al-Karkhi, ya fito domin ya gana da ita.

Mutum daya daga cikin danginsa da masu bashi kariya biyu suna cikin wadanda suka mutu a harin da aka kai a garin Kanaan,dake kudu maso gabashin Baquba fadar lardin na Diyala.

Al-Qaida tana kara yawan amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake a Iraqi. A jiya lahadi rundunar sojin Amurka a Iraqi tace jerin munanan hare hare a Iraqi ba alama ce ta cewa ana samun karuwar tashe tashen hankula bane a kasar.

XS
SM
MD
LG