Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A kai wasu hare haren kunar bakin wake a garin Lahore da ya kashe mutane ashirin da biyar


Mahukuntan kasar Pakistan sun ce wasu hare haren kunar bakin wake da aka kai kan wasu motoci biyu a garin Lahore daga gabashin kasar ya kashe mutane 25 ya kuma jikkata kimanin maitan yau.

Harin na farko ya lalata shelkwatar rundunar ’yan sanda ta ƙasa dake cikin gari, inda mutane 21 suka rasa rayukansu. Jami’ai sun ce a kalla goma sha biyu daga cikin mamatan ma’aikatan hukumar ’yan sanda ne.

Bayan dan lokaci kadan ne kuma wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa motarsa a kofar wani kamfanin tallace tallace dake dab da wasu gidajen kwana, nisan ’yan kilomita kalilan tsakaninsu da na farko. Jami’ai suka ce a kalla mutane hudu suka mutu a wannan harin da suka hada da kanannan yara biyu.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin. Babban jami’in ’yan sanda na birnin Malik Mohammaed Iqbal ya shaidawa manema labarai cewa harin ta’addanci ne. Ga Sahabo Imam Aliyu da fassarar rahoton da wakilinmu Steve Herman ya aiko mana daga Islamabad.

XS
SM
MD
LG