Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Zimbabwe sunce sunce 'yan sanda da sojoji dauke da manyan makamai sun bazu a fadin kasar kafin zaben da za a yi gobe asabar


Yan sanda da sojoji dauke da manyan makamai sun bazu a fadin kasar kafin zaben da za a yi gobe asabar. mazauna unguwannin dake bayangarin Harare, sun fada ma VOA cewa dakarun tsaro suna yin sintiri cikin motoci masu sulke, da na fesa ruwa da karfi har ma akwai wasu a kan babura.

Har ila yau, shaidu sun fada ma VOA cewa jiragen saman yaki suna yin shwagi kasa kasa a fadin kasar. A cikin wata hirar da yayi da jaridar Financial Times, madugun 'yan hamayya Morgan Tsvangirai ya gargadi shugaba Robert Mugabe da kada yayi kokarin satar wannan zabe.

Tsvangirai yace duk wani yunkurin yin hakan zai kara jefa wannan kasa cikin fitina. Mr. Mugabe yayi barazanar daukar matakai masu tsanani a kan 'yan hamayya idan suka kuskura suka yi adawa da sakamakon zaben da za a yin.

A jiya alhamis, 'yan jaridar kasashen waje sun yi tur da gwamnatin Zimbabwe a saboda ta ki ta kyale akasarin 'yan jarida su dauko rahotannin zaben.

XS
SM
MD
LG