Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyar shugaban adawa Morgan Tsvangirai na kasar Zimbabwe tana ikirarin nasara a zaben shugaban kasa


Jam’iyar shugaban adawa Morgan Tsvangirai na kasar Zimbabwe tana ikirarin nasara a zaben shugaban kasa da na ’yan majalisa da aka gudanar. Babban sakatare na jami’yar Movement for Democratic Change, Tendai Biti, yace bisa ga sakamakon zaben da aka lika a runfunan zabe, Mr. Tsvangirai ya sami kashi hamsin na kuri’un saboda haka babu bukatar gudanar da zaben fidda gwani.

Ya bayyana haka ne yau a wani taron manema labarai a Harare. Mataimakin ministan yada labarai na kasar Zimbabwe Bright Matonga wanda yake memban jam’iya mai mulki, ya musunta harsashen MDC.

Ya shaidawa BBC cewa mafarki ne jam’iyar NDC ke yi da da’awar nasarar, da cewa ya kamata su jira sakamakon zabe da hukumar zata bayar. Kafar sadarwa ta gwamnatin Zimbabwe tace sakamakon zaben da aka gudanar ranar asabar ya nuna cewa babu wanda ya sami sama da rabin kuri’un da aka kada tsakanin ’yan takarar saboda haka ya zama tilas a gudanar da zaben fidda gwani.

XS
SM
MD
LG