Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Fasinja Ya Fado Kan Mutane A Garin Goma A Kasar Kwango Ta Kinshasa


Jami’ai a kasar Kwango ta Kinshasa sun ce mutane fiye da saba’in suka mutu a lokacin da wani jirgin saman fasinja ya fadi a birnin Goma dake gabashin kasar.

Jami’ai suka ce jirgin, kirar DC-9 yana dauke da mutane har 100 a lokacin da ya subuto kan wani wuri mai kasuwa ya kama da wuta jim kadan a bayan tashinsa yau talata. Suka ce mutane akalla 6 a cikin jirgin sun kubuta da rayukansu, cikinsu har da biyu daga cikin matuka jirgin.

Shaidu sunce da alamun akwai wadanda suka mutu daga cikin mutanen da jirgin ya fado a kansu.

Jami’ai suka ce jirgin na kamfanin safarar jiragen sama na Hewa Bora, ya doshi Kinshasa ne, babban birnin kasar. A makon jiya, Kungiyar Tarayyar Turai ta saka sunan kamfanin safarar jiragen saman Hewa Bora a cikin wadanda ta haramtawa jiragensu shawagi a kasashen Turai a saboda damuwa kan lafiyar jiragen nasu.

XS
SM
MD
LG