Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe:Shugabannin ikilisiyan kasar China sun ce ana garkuwa da jama’a, ana gallaza musu azaba ko kuma a kashesu a wani sabon salon


Shugabannin ikilisiyan kasar China sun ce ana garkuwa da jama’a, ana gallaza musu azaba ko kuma a kashesu a wani sabon salon tursasawa babbar jam’iyar adawa da ake yi a kasar.

A cikin sanarwar da suka bayar yau, gamayyar ikilisiyan kirista sun yi kira domin kawo tallafin kasa da kasa, da cewa tashin hankali zai iya zama kisan kare dangi idan ba a dauki mataki ba. Makon jiya, kungiyar Human Right Watch tace jam’iya mai mulki ta ZANU-PF tana amfani da wasu dakunan tsare mutane na bayan fage, tana duka da kuma azabtawa magoya bayan jam’iyar Movement for Democratic Change.

Gwamnatin Zimbabwe ta musunta dukan zarge zargen haddasa tashe tashen hankali na siyasa. Jaridar Herald ta gwamnati ta ambaci ta bakin ministan harkokin shari’a na kasar yana cewa dukan wanda yake da masaniya game da irin wannan tashin hankalin ya tuntudi yan sanda. An fara tashin hankali ne jim kadan bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 29 ga watan Maris, da ake takaddama a kai. Jam’iyar MDC tace dan takararta Morgan Tsvangirai ne ya lashe zaben, sai dai har yanzu ba a fitar da sakamakon zaben ba, abinda ya sa ake zargin cewa Mr. Mugabe yana kokarin yin tazarce.

A halin da ake ciki kuma jami’an diplomasiya na amurka suna matsawa kasar Sin da kuma gwamnatocin afrika da dama lamba su hana shigar da makaman kasar China zuwa Zimbabwe. kakakin ma’aikatar harkokin wajen amurka Ton Casey yace amurka ta tattauna batun jirgin ruwan na kasar China da gwamnatin Beijing da kuma ta kasashen kudancin afrika da suka hada da Afrika ta Kudu, da Mozambique da Namibia da kuma Angola. Casey yace jami’an gudanarwa na gwamnati sun gamsu da jawabin ministan harkokin kasashen ketare na kasar Sin, cewa ya yiwu a maida jirgin China.

Jirgin ruwan na China yana gadar tekun Afrika ta kudu tun makon jiya yana neman inda zai sauke kayansa. An bashi izinin sauke kaya a tashar jirgin ruwan afrika ta kudu dake Durban ranar jumma’a amma ma’aikata a wurin suka bijerewa sauke makaman da aikawasu Zimbabwe domin gudun kada shugaba Robert Mugabe ya yi amfani da shi wajen tursasawa abokan hamayyarsa

XS
SM
MD
LG