Mai neman tsayawa takarar kujerar shugabancin Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Democrat, Barack Obama, ya ce ba ya da shirin daukar matakan bakanta abokiyar hamayyarsa, Hillary Clinton, a yayin da suka mayar da hankali ga sauran jihohin da suka rage a wannan takara.
A cikin hirar da yayi da wani gidan rediyo, Sanata Obama yayi watsi da rahoton da jaridar Washington Post ta buga cewar watakila zai buga tallace-tallace masu bakanta abokiyar hamayyar tasa. Yace yana son ya ci gaba da abinda ya saba na yin magana kan batutuwan dake addabar jama’a a yayin da yake kokarin shawo kan masu jefa kuri’a a jihohin Indiana da Carolina ta Arewa wadanda zasu gudanar da zabubbukansu ranar 6 ga watan Mayu.
Sanata Clinton ta doke Obama da kusan maki 10 a zaben da aka yi jiya talata a Jihar Pennsylvania. Clinton ta fadi yau laraba cewar wannan nasara ta nuna cewa zata iya gina harsashin da ake bukata na masu jefa kuri’a don lashe kujerar shugabancin Amurka.