Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yace zai shugabanci kwamiti na musamman wanda zai shawo kan matsalar tashin kayan masarufi suke


Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yace zai shugabanci kwamiti na musamman wanda zai shawo kan matsalar tashin gwauron zako da kayan masarufi suke yi a kasashen duniya.

Mr. Ban ya sanar da haka ne a bern Swtizerland, yau a wani taron kwana biyu da ya kunshi manyan cibiyoyin kasa da kasa ishirin da bakwai. Cibiyoyin suna neman gabatar da hanyoyin gaggawa na shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi dake haddasa yunwa, da tarzoma da koye cimaka a kasashen dake fama da talauci na duniya.

Nathan Childs wani kwararre ne a fannin noman shinkafa wanda ke aiki a ma’aikatar noma ta amurka. Yace yayinda hauhawan farashin man fetir da takin zamani ya haddasa tsadar kayan masarufi cikin shekaru biyu da suka shige, akwai wani bayani dangane da hauhawar farashin da kayayyaki suka yi shekaru cikin shekaru hudu da suka shige.

XS
SM
MD
LG