Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Kashe Dubban Mutane A Kasar Sin


Hukumomin Sin sun ce girgizar kasar da ta abku a lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar ta kashe dubban mutane.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin ya ce a wata karamar hukuma mai suna Beichuan kawai a lardin na Sichuan, mutane dubu uku zuwa dubu biyar ne suka mutu, kuma ana fargabar cewa mutane dubu goma ne suka ji rauni a wannan wurin kawai. Beichuan na da tazarar kimanin kilomita 160 a arewa da Chengdu, babban birnin lardin Sichuan.

Har ila yau kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ce girgizar kasar ta kuma lalata wasu masana'antun sarrafa magungunan kimiyya guda biyu, inda gine-gine suka binne daruruwan mutane, aka kuma kwashe dubban mutane ala tilas daga yankin.

Hukumar Nazarin Fasalin kasa ta Amurka ta ce wannan girgizar kasa mai karfin awu 7 da digo 8 a ma'aunin motsin kasa na Richter, ta faru da tsakar rana agogon kasar (misalin karfe 7 da minti 28 na safe agogon Nijeriya), kuma an ji hucinta a wurare masu nisa kamar tsibirin Taiwan da birnin Bangkok a kasar Thailand.

Hukumar ta ce idanun wannan girgizar kasa ta bulla a wani wuri mai tazarar kilomita 92 a arewa maso yamma da Chengdu a cikin karamar hukumar Wenchuan.

Haka kuma rahotanni sun ce wasu makarantun firamre guda biyu sun rushe suka binne dalibai kusan dari tara a wani gari a kusa da karamar hukumar at Wenchuan. Babu karin bayanin da aka samu kan wannan, kuma ba a san halin da daliban suke ciki ba.

Xinhua ya ce an tabbatar da mutuwar mutane da yawa a lardunan Sichuan, gansu, Yunnan, da kuma garin Chongqing.

XS
SM
MD
LG