Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sun Gano Cewa Sanata Edward Ted Kennedy Yana Dauke Da Cutar Sankara A Kwakwalwarsa


Likitocin Sanata Edward Ted Kennedy na Amurka sun bayyana cewa dan majalisar dattijan yana dauke da cutar sankara a kwakwalwarsa.

A cikin wannan makon, an rike Kennedy a wani asibiti a Jiharsu ta Massachussetts ana yi masa gwaje-gwaje don gano abinda ya sa ya gamu da fizgar zuciya ranar asabar. Likitoci sun ce zasu yanke shawara a kan irin jinyar da za a yi masa a bayan sun kara yin gwaje-gwaje.

Fadar White House ta ce shugaba George Bush yayi bakin ciki sosai da jin wannan labari na abinda ke damun lafiyar Kennedy, kuma zai ci gaba da taya shi addu’ar sauki.

Shugabar majalisar wakilan tarayyar Amurka, Nancy Pelosi, da sauran abokan aikin sanatan duk sun bayyana shi a zaman gwarzon namiji, suka kuma bayyana kwarin guiwar cewa zai yaki wannan cuta.

Sanatan dan jam’iyyar Democrat mai shekaru 76 da haihuwa, ya shafe shekaru fiye da 45 a cikin majalisar dattijan Amurka. Shi ne kanin marigayi shugaba John F. Kennedy, wanda aka kashe a 1963.

XS
SM
MD
LG