Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Guinea, sojoji sun harbe wani jami’in kula da kudadensu


Jami’ar rundunar sojin Guinea, sunce wadansu sojoji dake bukatar a biyasu wasu kudadensu, sun harbe wani jami’in kula da kudadens, har sun ji masa ciwo.

Jami’an sun fada a yau cewa sojojin sun raunata Manjo Korka Dioallo, a lokacin da suke wata zanga-zanga a babban birnin Guinea na Conakry. Zanga zangar ta barke ne tun a jiya Litinin, lokacin da sojojin suka rika harba harsashi a sama, a wani sansanin soji dake Conakry.

Sojojin tsohon Prime Minista Lansana Kouyate – wanda aka kora a makon da ya gabata, yayi masu alkawarin kimanin dollar dubu daya da dari daya da suke bi bashi.

XS
SM
MD
LG