Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aski Ya Zo Gaban Goshi Ga Masu Neman Jam'iyyar Democrat Ta Tsayar Da Su Takarar Shugabancin Amurka


A yau talata za a kammala zabubbuka masu kama da gudun-yada-kanin-wani na fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat a nan Amurka, inda masu jefa kuri’a na jihohi biyu kacal da suka rage zasu fitar da gwaninsu.

A bisa dukkan alamu, sanata Barack Obama ne zai lashe wannan takarar da ta yi zafi a tsakaninsa da sanata Hillary Clinton don zamowa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Amma da yake wakilan da za a yi takararsu guda 31 ne kawai a jihohin Dakota ta Kudu da Montana, Obama ba zai iya hayewa ta hanyar wakilan da ake takararsu a zabe kawai ba. Ma’ana, wakilai masu zaman kansu, ko Superdelegates a Turance, sune zasu yanke shawarar mutumin da zai yi nasara. Wakilai masu zaman kansu dai shugabanni ne da zababbun ’yan jam’iyyar wadanda suke da ikon goyon bayan kowane dan takarar da suek so a lokacin babban taron tabbatar da dan takara nan jam’iyya a watan Agusta.

Jami’an jam’iyyar Democrat sun ce su na tsammanin wakilai masu zaman kansu da yawa zasu bayyana goyon bayansu ga Obama a bayan rufe rumfunan zabe a yau talata. Suka ce yawan wakilan zai sa ya haye.

A yau talata da daddare, Obama yake shirin kaddamar da yakin neman babban zabe na shugaban kasa, inda zai gwabza da Sanata John McCain na jam’iyyar Republican, a wani gangamin da zai gudanar a jihar Minnesota.

A halin da ake ciki, kwamitin yakin neman zaben Uwargida Clinton ya nuna alamun cewa tafiya ta zo bakin gacci, ko kuma aski ya zo gaban goshi. Tsohon shugaba Bill Clinton ya fadawa magoya baya jiya litinin da daddare a Jihar Dakota ta Kudu cewa watakila wannan shi ne karo na karshe da zai shiga kyamfe irin wannan. Ya ce yana mai alfaharin yakin neman zabe ma uwargidar tasa. A jiya litinin kuma, an sallami wasu daga cikin ma’aikatan yakin neman zabe na Clinton.

A lokacin da ya yada zangon yakin neman zabe a Jihar Michigan, Obama ya yaba ma Uwargida Clinton. Har ila yau ya ce yana dokin zama da ita a duk lokaci da kuma wurin da ta zaba, yana mai yin alkawarin daukar dukkan matakan da zai iya don hada kan ’ya’yan jam’iyyar kafin babban zabe.

XS
SM
MD
LG