Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Mayakan Ruwan Nijeriya A Cikin Teku Kusa Da Gabar Kudancin Kasar


Majiyoyin tsaro da na man fetur a Nijeriya sun ce an kashe sojan ruwa guda daya, wasu suka ji rauni, a lokacin da ’yan bindiga suka kai farmaki a kan wani jirgin ruwa a teku dab da gabar kudancin kasar.

Jami’an sojan Nijeriya sun ce mayakan na ruwa su na tsaron wani dandalin tonon man fetur a cikin teku ne a lokacin da ’yan bindiga cikin kananan kwale-kwale masu gudu suka yi musu kwanton-bauna a yau litinin.

Kamfanin man fetur na Addax dake da wannan rijiyar tonon mai ya ce an kashe soja daya, wasu hudu kuma suka ji rauni a wannan harin. Ya ce wadanda suka ji raunin kuma, an dauke su zuwa babbar cibiyar mai ta Bonny domin jinya.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin. ’Yan tsagera a yankin Niger Delta su na yawaita kai hare-hare a kan cibiyoyin mai, a yunkurinsu na ganin an ware karin kason dukiyar mai ga al’ummar yankin. Amma kuma wasu hare-haren na masu fashi ne da kuma masu neman kudin fansa.

XS
SM
MD
LG