Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnatin Afghanistan Da Na NATO Su Na Yakar 'Yan Taliban A Kandahar


Jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce an kashe 'yan Taliban su fiye da 20 a kudancin kasar, inda sojojin NATO da na Afghanistan suka kaddamar da wani farmakin hadin guiwa kan 'yan tawayen.

Ma'aikatar tsaro ta Afghanistan ta ce an kashe jami'an sojanta biyu a lokacin wannan artabu a gundumar Arghandab, a arewa da birnin Kandahar. Da asubahin yau laraba aka kaddamar da wannan farmakin hadin guiwa wanda ya kunshi yin amfani da jiragen helkwafta na kai farmaki da manyan makamai.

Ma'aikatar tsaron ta fada jiya talata cewa daruruwan mayakan Taliban sun saci jiki suka shiga kauyuka da dama a kusa da Kandahar, amma daga baya ma'aikatar tsaron Amurka ta ce abin bai kai haka ba.

Dubban mutanen yankin sun gudu daga gidajensu cikin 'yan kwanakin nan. Jiragen saman NATO sun yi ta jefo kasidu inda a ciki ake kira ga jama'a da kada su fita waje idan fada ya barke.

Haka kuma a yau laraba, ma'aikatar tsaron Britaniya ta ce wani bam da aka boye a gefen hanya, ya tashi ya kashe mata sojoji hudu jiya talata a lardin Helmand dake kudancin kasar.

XS
SM
MD
LG