Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morgan Tsvangirai Ya Janye Daga Zaben Fitar Da Gwani Na Shugaban Kasa A Zimbabwe


Madugun hamayya na kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya janye daga zaben fitar da gwani na ranar jumma'a mai zuwa inda aka shirya zai gwabza da shugaba Robert Mugabe, yana mai fadin cewa magoya bayansa za su jefa rayukansu cikin hatsari idan suka fito jefa kuri'a.

Mr. Tsvangirai ya bayyana wannan lahadi, 'yan sa'o'i kadan a bayan da dubban matasa 'yan tsagera masu goyon bayan Mr. Mugabe suka hana magoya bayan jam'iyyar hamayya ta MDC hallara domin gudanar da gangamin yakin neman zabe a Harare, babban birnin kasar.

Mr. Tsvangirai yayi watsi da zaben a zaman haramtacce, kuma kazamin yunkurin yin rufa ido, yana mai zargin magoya bayan shugaba Mugabe da laifin kashe magoya bayan jam'iyyar hamayya ta MDC su tamanin da shida cikin 'yan makonnin nan.

Ba a dai ji martani daga bakin Mr. Mugabe nan take ba, amma ministan shari'a na Zimbabwe, Patrick Chinamasa, ya ce Mr. Tsvangirai ya janye ne a saboda ta tabbata cewa zai sha kaye.

haka kuma, jami'ai sun bayyana cewa za a gudanar da zaben kamar yadda aka shirya har sai Mr. Tsvangirai ya sanar da hukumar zabe cewa ya janye.

Mr. Tsvangirai ya ce a ranar laraba zai bayyana matakin da zai dauka a nan gaba.

XS
SM
MD
LG