Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Gasar Kacici-Kacici Ta 2008


Sashen Hausa na Muryar Amurka ya bayar da sanarwar sabuwar gasar Kacici-Kacici ta shekarar 2008, wadda a wannan karon za ta kunshi akwatunan rediyo mafiya inganci da wannan gidan rediyo ya taba bayarwa.

A lokacin da yake bayar da albishir ga masu sauraron Sashen Hausa a birnin Washington, shugaban wannan sashe, Sunday Dare, ya ce a wannan karon kuma, za a tattara kyaututtukan a wuri guda domin gujewa matsalolin da aka fuskanta a baya, inda wasu masu sauraro suka lashe kyaututtuka, amma kuma kyaututtukan suka bace a hanya. (Wadanda kyaututtukansu suka bata ana kan kokarin samar musu da wasu kyaututtukan a bisa sanarwar da Mr. dare ya bayar).

Shugaban na Sashen hausa ya ce a wannan karon, duk wanda ya lashe akwatin rediyo, zai karbi kyautarsa kai tsaye daga ofishin huldar jakadanci na Amurka dake birnin Abuja. Wanda ba zai iya zuwa ba, yana iya tura takardar shaidarsa a ba shi.

A wannan karon dai, za a raba kyaututtukan akwatunan rediyo samfurin Eton E5 ne. Shi wannan akwatin rediyo, yana da kaifin kamo tasha, kuma yana iya kamo duk wata tashar rediyo har ma da mitocin da jiragen sama ke magana kansu idan su na tafiya a sama.

Gasar ta bana, in ji Mr. Dare, zata maida hankali ne kan shirin da Sashen Hausa ke gabatarwa da karfe 9.30 na dare agogon Nijeriya, shirin da aka kara masa kuzari ta hanyar karkata shi ya zamo dandali na ra'ayoyin masu sauraro kan abubuwan da suke gudana a rayuwarsu da shugabanninsu.

Daga wannan makon, har zuwa karshen watan Yuli, sai a saurari shirin na dare. A karshen wata, za a yi tambaya dangane da wani abinda za a ji cikin shirin na dare. Duk wanda ya amsa tambayar daidai, to yana iya lashe akwatin rediyo.

Idan har aka samu wadanda suka amsa tambayar daidai fiye da yawan kyaututtukan da ake da su, to, kamar yadda aka saba, za a rufe idanu a dauko takardu daidai yawan kyaututtuka daga cikin wadanda suka amsa daidai.

Allah Ya ba da mai rabo sa'a.

XS
SM
MD
LG