Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Maganin Tarin Fuka Yana Rage Karfin Maganin Kashe Kaifin Cutar Kanjamau


Wani sabon binciken da aka wallafa jiya lahadi a Mujallar Kungiyar Likitoci ta Amurka ya nuna cewa marasa lafiyar da aka yi ma jinyar tarin fuka ba za su ci moriyar magungunan dakushe karfin kwayar cutar HIV mai haddasa kanjamau ba.

Wannan bincike ya gano cewa maganin nan mai arha da ake kira "Nevipirine" wanda ake amfani da shi wajen yakar kwayar cutar HIV a kasashe masu tasowa, ba ya aiki sosai a jikin mutanen da suke shan maganin tarin fuka.

Maganin kashe kwayoyin cutar nan mai suna "Rifampicin", wanda a lokuta da dama ake yin amfani da shi wajen jinyar masu fama da tarin fuka, yana rage yawan maganin "Nevipirine" a cikin jini. Amma kuma, an gano cewa babu wata alamar cewa maganin na tarin fuka yana rage karfin wani maganin yakar kwayar cutar HIV mai tsada da ake kira "Efavirenz".

XS
SM
MD
LG