Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Kimiyya Sun Gano Kaburburan Mutanen Zamanin Da Cikin Hamadar Sahara A Nijar


Wata kungiyar masu tonon binciko abubuwa na tarihi dake karkashin jagorancin Amurka ta ce ta gano wasu kayayyakin tarihin zamanin da a cikin hamadar Sahara a kasar Nijar.

Masana kimiyya suka ce wurin ya kunshi wata makabarta dauke da kasusuwan mutane. Sun kuma gano kasusuwan wasu manya-manyan kifaye da kadduna.

Iskar hamada mai zafi ta tono wannan makabarta har aka gano ta a cikin Sahara, a wani wurin da shekaru dubu goma da suka shige, fadama ce mai ni'ima.

Masana kimiyyar sun gano wadannan a lokacin da suke neman kasusuwan manya-manyan dabbobin zamanin da, wadanda ake kira "Dinosaur" a turance a wannan bangare na hamadar Sahara da Abzinawa suke kira hamada a cikin hamada.

Daya daga cikin abubuwan ban mamaki da masana suka gano a wurin shi ne kashin wata mace, fuskarta na kalon kasusuwan wasu yara kanana su biyu, tamkar tana rungume da su. Ire-iren tsirrai da aka gano a cikin kabarin ya nuna cewar an binne su a kan furanni, shekaru dubu biyar da suka shige.

XS
SM
MD
LG