Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon firayim ministan kasar Pakistan ,Nawaz Sharif, ya yanke sabon lokacin dawo da manyan alkalan kasar


Tsohon firayim ministan kasar Pakistan ,Nawaz Sharif, ya yanke sabon lokacin dawo da manyan alkalan kasar, alamarin dake wa mulkin hadin gwiwar kasar barazana.

Bayan da suka tatauna da kananan jamiyyun mukin hadin gwiwan, Mr sharif ya fada a yau jummaa cewa zaa kaddamar da yarjejeniyar maida alkalan da tsohon shugaban kasar Pervez ya kora daga aiki, wa yan majalisan dokoki ,don su jefa kuria ranar litini.Ya kara da cewa yana saran cewa alkalan zasu koma bakin aiki nan da kwanabiyu.

A wata sabuwar kuma ,yan sanda Pakistan sun ce sun kama wanda suke zargin shine dan-kunar-bakin wake na uku a harin da ya kashe akalla mutane sittin da hudu a kusa da garin Islamabad.

Yan sandan sun kara da cewa, sun kwace wani riga dake dauke da nakiyoyi a wata masallaci kusa da babban masana’antar makamai da aka kaima hari a garin Wah.

XS
SM
MD
LG