Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michelle Obama, matar dan takaran jam’iyyar Democrat, ta  gayawa mahalarta taron cewa Obama zai zamar wa Amurka hazikin shugaba


A daren jiya ne shugabannin jam’iyyar Democrats suka fara gagarumin babban taronsu na yin abin tarihin tsaida baker fata na farko a tarihin Amurka da wata babbar jam’iyya zata tsaida yayi mata takaran shugaban kasa – watau Barack Obama.

A wajen taron da ake a birnin Denver na jihar Colarado, anyi jawabban jinjinawa daya daga cikin ginshikan ‘yan siyasar Amurka, Sen. Edward Kennedy.

Daga baya ne kuma Michelle Obama, matar shi dan takaran, ta fito tana gayawa mahalarta taron cewa Obama zai zamar wa Amurka hazikin shugaba. Ta gayawa tron cewa ita da Barack Obama ‘yayan talakawa ne kamar milyoyin Amurkawa da suka tashi cikin darajar iyali da mutunta kowa suka ci karo da shi

XS
SM
MD
LG