Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A yammacin Alhamis din nan ne, dan takarar shugabancin Amurka na Jam’iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na’am da tsaida shi dan takara


A yammacin Alhamis din nan ne,ake sa ran dan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na'am da tsaida shi dan takara, a jawabi da ake doki zai gabatar,wanda kuma zai kawo karshen babban taron Jam'iyyar.

Obama zai yi jawabi ga dubban mutane a wani dandalin wasanni mai suna "Mile High Stadium",a birnin Denver,cikin Jihar Colorado, dake yammacin Amurka.

Cikin sanannun Jam'iyyar har da zasu yi jawabi ga gangamin har da tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Al Gore,da kuma Gwamnan Jihar New Mexico,Bill Richardson, Haka kuma za a nunawa wakilai majigi kan tsohon shugaban rajin kare hakkin bil'adama, Martin Luther King,wadda yau ce cikar shekaru 45 da gabatar da fitaccen jawabin sa,da aka lakabawa suna "Ina Mafarki".

Jiya Laraba da dare ne taron ya tsaida Obama da mataimakin sa Joseph Biden.Obama ne bakar fatar Amurka na farko da wata babbar Jam'iyyar siyasa ta tsayar takarar shugabancin Amurka. A jiyan tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ya kira Obama,mutumin da ya dace da aikin shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG