Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa


Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa,wanda yayi fice a tarihi, kuma ya shiga yakin neman zaben shugaban kasa na tsawon wata biyu a matsayin bakar-fatar Amurka na farko da rike tutar shugabancin babbar jamiyya.

Sanata Obama da abokin takarar sa ,Sanata Joe Biden,a yau juma'a zasu tafi jahar Pennsylvania,dake arewacin Amurka akan bos da zai yawata da su manyan jahohi.

A daren alhamis, Obama ya bayyana gaban jama'a fiye da dubu tamanin,suna masa tafi da shewa,inda yayi alkawarin kawo canji a kasar Amurka ya kuma bayyana banbancin sa da dan hamayyar sa na jamiyyar republican,Sanata John Mccain.

XS
SM
MD
LG