Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Jam’iyyar Republican ta Amurka zata fara aiwatar da shirye shiryen taron ta na kasa gadan gadan


Jam'iyyar Republican ta Amurka zata fara aiwatar da shirye shiryen taron ta na kasa gadan gadan ,bayan da guguwar teku mai karfi ta(Gustav) ta sanya Jam'iyyar takaita shirye shiryen ta a yinin farko jiya litinin.

Kamfanonin dillancin labaru sun bada labarin watakil shugaba Bush zai yi jawabi ga gangamin daga Fadar white House ta tauraruwar dan Adam.Ya soke halartar taron jiya litinin domin ya maida hankali wajen ganin yadda Gwamnatin tarayya take tafiyar da ayyukan agazawa yankin da guguwar Gustav ta rutsa.

Tsohon magajin garin N/Y Rudy Gulianai,wadda shima yayi takarar neman a tsaida shi shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar ta Republican zai gabatar da jawabi na musamman ga gangamin a yau Talata.

John Mccain,wadda cikin makon nan ne zai yi jawabin amincewa da tsaida shi takarara,jiya litinin ya wuni ne a Jihar Ohio dake tsakiya maso yammacin Amurka inda ya maida hankali kan guguwar Gustav wacce ta fatattaki yankuna dake dab da gaba. Uwargidan John Mccain,tareda uwargidan shugaba Bush Laura, sunyi jawabai ga takaitaccen taron inda suka bukaci mahalarta su jingine siyasa su bada gudumawa ga ayyukan jinkai.

XS
SM
MD
LG