Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Daren Alhamis Din Nan ne Masu Takarar Mataimakan Shugaban Kasar Amurka Biden da Palin Zasu Kara a St Louis Dare Alhamis Din Nan


Dan Majalisar Dattijan Amurka, Democrat Joe Biden,da Gwmamnan Alaska,Republican Sarah Palin, zasu kara Alhamis din nan,a muhawara daya rak tsakanin masu takarar mataimakan shugaban kasa.

Ana sa ran matsalar Tattalin Arziki zata zame babban batu a muhawarar da za a yi a St. Louis,Missouri,kuma za a maida hankali ainun kan Palin wacce kusan bakuwa ce sisayar kasa.

Daukar Sarah Palin a matsayin mataimakiyar shugaban kasa da dan takarar shugabancin Amurka John Mccain na Republican yayi ya tsuma magoya bayan Jam’iyyar masu ra’ayin rikau,amma masu suka suna shakkar ko tana da kawarewar zama mataimakiyar shugaban kasa. Mccain a hira da yayi da tashar talabijin na CNN a yau,ya kare Sarah palin,kuma yace yana da kwarin gwiwa kan kwarewa da shugabancin ta.

Palin zata kara da tsohon hanu a Washington, Senator Joe Biden,daga Deleware,wadda matsalar sa itace tabka kura kurai.

XS
SM
MD
LG