Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Da McCain Su na Yakin Neman Zabe Na Karshe A Jajiberen Zabe


A nan Amurka, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat, Barack Obama, da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Republican, John McCain, su na yakin neman kuri'u na karshe a yau litinin, inda za su gudanar da tarurruka masu yawa a jihohin dake da muhimmanci ga lashe zaben.

Sanata McCain zai kai gwauro da mari a jihohi guda bakwai a yau litinin, inda zai faro daga Jihar Florida, ya kuma kammala da wani gangami da tsakar dare a Jiharsa ta Arizona. Shi dai McCain yana hankoron wasu jihohi ne da dan'uwansa dan jam'iyyar Republican, shugaba George Bush, ya lashe shekaru hudu da suka shige, amma kuma zai yada zango a muhimmiyar jihar na ta Pennsylvania wadda John Kerry na Democrat ne ya lashe shekaru hudu da suka shige. Dukkan 'yan takarar biyu sun kai ziyara sau da dama zuwa Jihar ta Pennsylvania a cikin 'yan makonnin nan.

Sanata Obama zai yi yakin neman zabe a wasu muhimman jihohi guda uku, watau Virginia da Carolina ta Arewa da Florida, wadanda Mr. Bush ya lashe a 2004, amma kuma a bana, ana ganin alamun cewa jam'iyyar Democrat tana iya lashewa. Wadannan jihohi uku su na da wakilai 55 daga cikin 270 da dan takara yake bukata domin zamowa shugaban kasa a nan Amurka. A tsarin zabe na Amurka, ana yin takarar wakilan zaben shugaban kasa na kowace jiha ce, wadanda su ne daga baya za su zo su kada kuri'ar zaben shugaban kasa.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a na kasa sun nuna cewa sanata Barack Obama ne yake kan gaba da rata mai 'yar tazara ana dab da zaben na gobe talata.

XS
SM
MD
LG