Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Sun Zabi Barack Obama


Amurkawa sun zabi bakar fata na farko a zaman shugabansu.

Barack Obama, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat, ya samu wakilai fiye da 270 da ake bukata a zaben da aka gudanar jiya talata,

Dubban magoya bayan Obama a garinsu, Chicago, sun barke da sowa ta murna a bayan da gidajen telebijin suka ayyana Barack Obama a zaman wanda ya lashe zaben.


Kokarin John McCain na lashe wannan zabe ya gamu da cikas a bayan da ya sha kaye a wasu muhimman jihohin da tilas ya lashe su idan yana son cin zabe, cikinsu har da Pennsylvania, Florida, Ohio, da kuma Virginia. babu wani dan takara na shugaban kasa na jam'iyyar Democrat da ya lashe Jihar Virginia tun shekarar 1964.

Nasarar da Barack Obama ya samu ita ta kawo karshen mulkin shekaru takwas na jam'iyyar Republican a karkashin jagorancin shugaba George Bush.

Za a rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu, 2009.

XS
SM
MD
LG