Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba George Bush Ya Kai Ziyarar Ba-Zata Zuwa Iraqi


Shugaba George Bush na Amurka yayi tattaki zuwa Iraqi domin in ban kwana da sojojin Amurka da shugabannin Iraqi. Mr. Bush ya sauka Bagadaza lahadi cikin matakan tsaro masu karfi, inda ya gana da shugaba Jalal Talabani na Iraqi.

Daga bisani ya fadawa 'yan jarida cewa yakin Iraqi mawuyaci ne, amma kuma ya zamo dole domin tabbatar da tsaron Amurka, da karfafa fatar Iraqi da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Wannan shi ne karo na hudu da Mr. Bush yake ziyarar Iraqi tun lokacin da ya tura sojojin Amurka da na kasashen kawance zuwa kasar a 2003.

Sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, wanda shi ma yake ziyara a Iraqi, ya fadawa sojojin Amurka a arewa da Bagadaza cewa aikinsu ya shiga matakin karshe. Ya ce a karkashin sabuwar yarjejeniyar tsaron da Amurka da Iraqi suka kulla, sojojin Amurka zasu bar birane da garuruwan Iraqi nan da karshen watan Yuni.

Gates ya ce nan da karshen watan Yuni, sojojin Amurka za su mika iko a dukkan larduna 18 na kasar Iraqi ga hukumomin kasar. Yace sannu da sannu sojojin Iraqi zasu ringa karbar karin ayyukan tsaro.

XS
SM
MD
LG