Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama Ya Zabi Wasu Jigogin Harkokin Kudi Don Tallafawa Tattalin Arziki


Shugaban Amurka mai jiran gado, Barack Obama, ya zabi wasu mutane uku da suka jima su na aikin kayyade harkokin kudi wadanda ya ce zasu taimaka wajen kafa sabbin ka'idojin da zasu kare tattalin arzikin Amurka.

A yau alhamis Mr. Obama ya zabi Mary Schapiro domin ta shugabanci Hukumar Sanya Idanu Kan Hada-Hadar Kudade Da Hannayen Jari. Ya ce za ta taimaka ta hanyar wanzar da sabuwar dabi'ar aiki tukuru tsakani da Allah a hukumar.

Ana sukar wannan hukuma sosai saboda sakacin da mutane da yawa suka ce ta nuna wajen sanya idanu a kan kamfanonin hada-hadar kudade a kasuwannin ahnnayen jari na Amurka kafin rushewar manyan bankunan zuba jari. Har ila yau, an zargi hukumar da ke kira "SEC" a takaice da laifin yin kunnen-kashi da gargadin da aka sha yi mata game da asusun zuba jari na zamba da ake zargin wani hamshakin dan kasuwa mai hada-hadar kudade, Barnard Madoff, da gudanarwa.

Shugaban na Amurka mai jiran gado ya kuma nada tsohon jami'in baitulmali Gary Gensler domin ya shugabanci hukumar da take kula da hada-hadar kasuwar haja ta Amurka. Har ila yau, Mr. Obama ya zabi wani shaihin malami na shari'a, kuma mai bada shawara ga tsohon shugaba Bill Clinton, domin yayi aiki a majalisar gudanarwar babban bankin Amurka.

XS
SM
MD
LG