Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba George Bush Zai Bada Rancen Dubban Miliyoyin Daloli Ga Kamfanonin Kera Motoci Na Amurka


Shugaba George Bush zai bada rancen dubban miliyoyin daloli ga kamfanonin kera motoci na Amurka da suka shiga cikin tasku, amma kuma ya bukace su da su yi wasu sauye-sauye masu wuya.

Gwamnatin Amurka ta gabatar da tayin bada kamfanonin rancen dala miliyan dubu 13 da miliyan 400 nan da 'yan kwanaki, sannan kuma zata ba su karin dala miliyan dubu 4 a cikin watan Fabrairu.

Mr. Bush ya ce tilas ne kowane bangaren da ya shafi masana'antar kera motoci, kama daga ma'aikata da shugabanni da masu binsu bashi da sauransu, su yi rangwame domin wannan shirin bada rancen yayi aiki. Tilas kamfanonin su rage albashin ma'aikata, su sayar da jiragen saman da shugabanninsu ke yawo ciki, su kuma biya masu kudaden fenshonsu da hannayen jari maimakon da tsabar kudi.

Shugaban Amurka mai jiran gado, Barack Obama, ya ce bada rancen ya zamo dole domin kaucewa abinda ya kira "mummunan sakamako ga tattalin arzikinmu da ma'aikatanmu." A cikin wata sanarwa ga 'yan jarida, yayi kira ga kamfanonin da kada su watsar da wannan dama ta sauya alkiblar gudanar da kamfanoninsu tare da ceto masana'antun da kuma miliyoyin ayyukan da suka dogara kansu.

XS
SM
MD
LG