Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Tura Karin Sojoji Zuwa Bakin Iyakarta Da Indiya


Jami'an Pakistan sun ce rundunar sojojin kasar tana tura dakaru zuwa bakin iyakarta da Indiya a saboda karuwar tankiya tsakanin kasashen biyu dangane da hare-haren ta'addancin da aka kai birnin Mumbai a watan da ya shige.

Shaidu sun ce daruruwan sojoji sun nausa gabas suka doshi bakin iyaka da kasar Indiya, daga inda aka girka su a bakin iyaka da Afghanistan inda suke yakar 'yan Taliban da al-Qa'ida.

Rundunar sojojin Pakistan ba ta fito ta tabbatar da sake ma sojojin bakin daga ba. Amma jami'an tsaron kasa sun ce rundunar ta soke hutun dukkan sojojin kasar, ta kuma sanya sojojin kasa da na sama cikin shirin ko-ta-kwana.

Tankiya ta karu sosai a tsakanin Pakistan da makwabciyarta Indiya tun bayan hare-haren da aka kai Mumbai. Indiya ta ce tsageran da suka kai harin 'yan Pakistan ne, sun kuma samu horaswa da makamai daga wata kungiyar 'yan tsagera mai cibiya a Pakistan. Pakistan ta nemi da a ba ta shaidar asalin kasar maharan.

A wani lamari makamancin wannan kuma, kasar Bangladesh ta ce ta tura jiragen ruwan yaki guda biyu zuwa wani yankin ruwan da ake gardama kansa a mashigin ruwan Bengal. Bangladesh tana rikici da Indiya kan batun binciken man fetur a wannan yanki.

Jami'an rundunar mayakan ruwan Bangladesh sun ce sun dauki wannan mataki a yau Jumma'a ne a bayan da Indiya ta tura jiragen ruwanta yankin, a bisa dukkan alamu domin binciken man fetur.

XS
SM
MD
LG