Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ce Lokacin Tsagaita Wuta Bai Zo Ba Tukuna


Majalisar zartaswar tsaro ta bani Isra’ila ta ki yarda da shawarar da kasashen duniya suka bayar cewa ta dakatar da farmakin sojan da take kaiwa kan Hamas a Zirin Gaza.

Wani kakakin Isra’ila, ya fadawa Muryar Amurka cewa ministoci da dama sun nazarci shawarwari dabam-dabam da kasashen duniya suka bayar kan tsagaita wuta, sun kuma yanke shawarar cewa babu wani jami’in kungiyar Hamas da zasu iya tattaunawa da shi.

Wani jami’in Isra’ila dake ambaton firayim minista Ehud Olmert, ya ce lokacin tsagaita wuta bai yi ba, amma kasar ta yahudawa zata nazarci kulla hakan nan gaba idan har yin haka zai kara tabbatar da tsaron kudancin Isra’ila.

A rana ta biyar a jere a yau laraba, jiragen saman yakin Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a kan cibiyoyin Hamas a Zirin Gaza. Makamai masu linzami sun abka kan gine-ginen gwamnati na Hamas da ramukan karkashin kasa da ake amfani da su wajen satar shiga da abinci da makamai zuwa Gaza daga Masar.

Hamas kuma ta ci gaba da cilla rokoki zuwa kudancin Isra’ila.

Falasdinawa kusan dari hudu aka kashe a wadannan hare-haren da Isra’ila take kaiwa ta sama. MDD ta ce akwai fararen hula akalla sittin da biyu a cikin wadanda aka kashe. An kashe ‘yan Isra’ila hudu, cikinsu har da fararen hula 3, a hare-haren rokoki da Falasdinawa ke kaiwa.

XS
SM
MD
LG