Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Yaran Dake Mutuwa A Sanadin Cutar Kyanda, Ko Bakondauro, Ya Ragu Da Kashi 74 Cikin 100.


Jami’an kiwon lafiya na duniya sun ce daga shekarar 2000 zuwa 2007, yawan wadanda ke mutuwa daga cutar kyanda a fadin duniya ya ragu daga dubu 750 a shekara, zuwa dubu 197. A daidai wannan lokacin, yawan wadanda ke mutuwa daga cutar a yankin gabashin tekun Bahar Rum, ya ragu daga dubu 96 a shekara zuwa dubu 10 kawai.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, tana da gurin rage yawan wadanda ke mutuwa a sanadin cutar kyanda da kimanin kashi 90 daga cikin 100 nan da karshen shekarar 2010. Tuni kasashen Afghanistan da Pakistan da Somaliya da kuma Sudan suka cimma wannan guri, yayin da wasu kasashen ma suke shirin cimma wannan gurin.

Sai dai Peter Strebel na hukumar WHO yayi gargadin cewa bai kamata masu yaki da cutar kyanda su yi sako-sako ba. Strebel ya ce, “Tilas kasashe su shirya, su kuma kasafta kudi na gudanar da aikin rigakafin cutar kyanda a fadin kasashen lokaci-lokaci domin tabbatar da cewa an kare dukkan yara.”

Strebel ya ce a kowace rana, yara 500 suke mutuwa daga wannan cuta, wadda ana iya kare ta cikin sauki ta hanyar rigakafi. Yawancin wadanda ke mutuwa daga cutar, yara ne ’yan kasa da shekara biyar da haihuwa.

Jami’an kiwon lafiya na duniya sun ce cutar kyanda ta fi yin kanta yanzu haka a kasar Indiya, inda kokarin kawar da cutar ke can kashin baya. Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta bayar sun nuna cewa a cikin shekaru takwas da suka shige, an rage yawan wadanda ke mutuwa daga cutar kyanda a kasar Indiya da kashi 67 cikin 100. A shekarar da ta shige, jami’ai sun ce mutane kimanin dubu 130 suka mutu a sanadin cutar kyanda a kasar Indiya.

Sai dai kuma, Edward Hoekstra na Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kasar ta Indiya za ta fara zafafa ayyukanta na allurar rigakafin cutar kyanda.

XS
SM
MD
LG