Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza


Sojojin kasa na Isra’ila tare da tallafin jiragen helkwafta na kai farmaki sun kutsa can cikin zirin Gaza, suka raba yankin na Falasdinawa dake bakin teku gida biyu.

Ma’aikatan jinya a asibiti sun ce an kashe Falasdinawa su fiye da talatin, akasarinsu fararen hula, yau lahadi a yayin da sojojin bani Isra’ila da na Hamas suke ba-ta-kashi a kan tituna. Rundunar sojojin bani Isra’ila ta ce an ji rauni ma sojojinta 30.

Wani kakakin firayim minista Ehud Olmert na Isra’ila ya fada ma gidan telebijin na al-Jazeera cewa Isra’ila zata ci gaba da wannan farmakin har sai an samu hanyar cimma zaman lafiya mai dorewa.

Cikin daren asabar Isra’ila ta umurci sojojinta na kasa da su kutsa cikin Gaza a bayan da ta shafe mako guda tana kai farmaki ta sama a kan yankin. Jami’an sojan Isra’ila suka ce ba aniyarsu ce su sake mamaye Gaza ba, su na so ne su lalata dukkan cibiyoyin Hamas a wannan yanki.

‘Yan kishin Hamas sun cilla rokoki kimanin 25 daga maraicen asabar zuwa safiyar lahadi a kan kudancin Isra’ila. Roka guda ta fada kan wani gini a birnin Ashdod ta ji rauni wa mutane biyu.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ban Ki-moon, yayi kira ga Isra’ila da ta ja burki ma wannan farmaki nata na sojojin kasa. Amma kuma Kwamitin Sulhun MDD ya kammala taron gaggawa da ya fara da maraicen asabar ba tare da cimma daidaituwa kan lamarin ba. Jami’an diflomasiyya suka ce Amurka ta sa kafa ta toshe hanyar amincewa da wani kudurin da kasar Libya ta gabatar dake kiran da a kawo karshen wannan fada nan take.

Jami’ai sun ce an kashe Falasdinawa akalla 500 tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare.

XS
SM
MD
LG