Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bird Flu


A yau laraba kasar Sin ta bayar da takardar gargadi game da cutar murar tsuntsaye, bayan da cutar ta kashe wata mace, sannan ta rufe kasuwannin sayar da kaji domin yi musu feshin kashe kwayoyin cutar a wani lardin dake kusa da birnin Beijing. Wannan mace ita ce ta farko da cutar ta kashe a kasar Sin a cikin shekara guda.

Matar, mai shekaru 19 da haihuwa, ta mutu a sanadin kwayar cutar murar tsuntsaye ta H5N1, a bayan da ta taba kaji a lardin Hebei. Wannan shi ya kawo adadin mutanen da cutar ta kashe a kasar Sin zuwa 21 ya zuwa yanzu.

A garin Yanjiao inda matar ta sayi agwagi a lardin Hebei, an rufe kasuwannin sayar da dabbobi dangin tsuntsaye, aka dakatar da sayar da su yayin da ma’aikata sanye da fararen kaya, kuma da fuska a rufe, suka bi su na fesa maganin kashe wkayoyin cutar.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce da alamu wuri guda kawai wannan abu ya shafa. Cikin wata sanarwar da ta bayar, hukumar ta ce, “babu shakka muna damuwa kwarai a duk lokacin da wannan kwayar cutar murar tsuntsaye ta kama wani mutum, amma kuma wannan lamari da ya faru (a Hebei) lokacin yankawa da kokarin dafa agwagwa, bai canja hasashen da muka yi tun farko kan wannan cuta ba.”

Kwayar cutar murar tsuntsaye ta fi yaduwa lokacin sanyi a tsakanin watannin Oktoba zuwa Maris, koda yake bullar kwayar cutar a kasar Sin ta nuna alamun sako-sako wajen kula da bullarta a jikin kaji ko agwagi. Kakakin ma’aikatar kiown lafiya ta kasar Sin, Mao Qunan, ya fadawa kafofin labarai na kasar cewa gwamnati zata kara kaimin sanya idanu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sin na Xinhua, ya ce a Beijing, babban birnin kasar, ma’aikata sun yadu domin bincike a kasuwannin sayar da dabbobi dangin kaji da gidajen yanka su a bayan da gwamnati ta bayar da takardar kashedin bullar cutar.

XS
SM
MD
LG