Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe yayi barazanar tsinke tattaunawar raba iko idan har shugaban 'yan hamayya Morgan Tsvangirai ya ki yarda da mukaman da za a ba bangarensa a ganawar da za a yi litinin din nan.
Kafofin labarai na gwamnatin Zimbabwe sun ambaci Mr. Mugabe yana fada lahadi cewa, "ko dai su amince da abinda za a ba su, ko kuma iyakar lanmarin ke nan." An shirya mutanen biyu zasu gana litinin.
Morgan Tsvangirai, shugaban jam'iyyar hamayya ta MDC, ya sanya hannu a kan yarjejeniyar raba iko da Mr. Mugabe a watan Satumba. Amma an kasa aiwatar da yarjejeniyar a saboda sabanin ra'ayi a kan yadda za a raba muhimman ma'aikatu a tsakaninsu.
Mr. Tsvangirai ya doke Mr. Mugabe a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Maris. Amma gwamnatin Mr. Mugabe ta ce bai samu fiye da rabin dukkan kuri'un da aka jefa ba, saboda haka ta ce a sake gudanar da zaben fitar da gwani a watan Yuni. Tsvangirai ya janye daga zaben na fitar da gwani, yana mai fadin cewa ana kashe magoya bayansa da yawa.