Mawaka da dama, kama daga amurka zuwa Turai zuwa Asiya da kasashen yankin tekun Carribean, sun yi ma sabon shugaban Amurka, Barack Obama, wakoki dabam-dabam na yabo da karrama abin tarihin da yayi.
Wata Bahaushiya ma, ta ce ba za a barta a baya ba.
A'ishatu Abdullahi Bauchi dai ba bakuwa ce a wurin masu sauraron wakokin Hausa ko kuma masu sauraron gidan rediyon Freedom FM ba. A shekarun baya, malama A'ishatu tana gabatar da wani shiri na musamman kan mawakan Hausa tare da shahararren mawakin nan, Mudassiru Kassim, a gidan rediyon na Freedom.
Mawakiyar ta rera wata waka ma shi Barack Obama, wakar da za a iya sauraro ko kofe idan aka duba gefen dama a saman wannan labari. A sha waka lafiya.