Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ethiopia Ta Ce Ta Kammala Janye Sojojinta Daga Somaliya


Ethiopia ko Habasha, ta ce ta kammala janye sojojinta daga Somaliya, inda aka tura su shekaru biyu da suka shige domin tallafawa gwamnatin riko ta kasar wajen yakar ‘yan tawaye masu kishin Islama.

Ministan sadarwa Bereket Simon, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa rundunar sojojin Ethiopia ta samu nasarar kammala ayyukanta a Somaliya, ta kuma janye dukkan sojojinta. Ya ce Ethiopia zata ci gaba da bayar da agaji ga gwamnatin Somaliya.

Ba a san yawan sojojin da kasar Ethiopia ta yi hasara a lokacin zamansu a Somaliya ba, amma an kashe dubban ‘yan Somali a fadan da aka yi ta yi kusan kowace rana a Mogadishu, babban birnin kasar.

Ethiopia ta fara janye sojojinta a farkon wannan wata, kimanin makonni goma a bayan da gwamnatin Somaliya ta cimma yarjejeniya da masu kishin Islama masu sassaucin ra’ayi.

A yau lahadi daruruwan ‘yan siyasa na Somaliya suka fara taro a kasar Djibouti domin kirkiro da sabuwar majalisar dokoki mai karin kujeru da aka tanada a cikin yarjejeniyar. Daga nan ne sabuwar majalisar zata zabi sabon shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG