Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsvangirai Yace Zimbabwe Tana Bukatar Sulhu Tsakanin Al'ummarta...


Sabon firayim ministan Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya ce kasar tana bukatar sulhu tsakanin al'ummarta da kuma tallafin al'ummar kasashen waje.

Mr. Tsvangirai ya fadawa magoya baya a garin Gweru mai tazarar kilomita 220 a kudu da Harare, babban birnin kasar, cewa kafa gwamnatin hadin kan kasa ita ce hanya daya tak ta warware rikicin da kasar ke fuskanta. An yi wannan gangami domin tuna cikar shekaru 10 da kafa jam'iyyarsa ta MDC.

Ya ce shugaba Robert Mugabe na jam'iyyar ZANU-Pf da kuma mukaddashin firayim minista Arthur Mutambara na wani bangaren jam'iyyar MDC da ya balle, su na rungumar yarjejeniyar raba ikon mulki.

A makon jiya Mr. Tsvangirai ya ce watakila Zimbabwe za ta bukaci dala miliyan dubu 5 na dogon lokaci domin farfadowa. Kasar tana fuskantar bala'i na tashin gwauron zabin da farashin kayayyaki ke yi, da rashin aiki da kuma rashin kayan bukatu.

XS
SM
MD
LG