Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Tarayyar Afirka  11 A Somaliya


Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta ce an kashe sojojin kiyaye zaman lafiya ‘yan kasar Burundi su 11 jiya lahadi, a lokacin da ‘yan tawaye suka kai farmaki kan wani sansanin ‘yan kiyaye zaman lafiya a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

Wata sanarwar da shugaban majalisar zartaswar kungiyar ta AU, Jean Ping, ya bayar, ta ce wasu ‘yan kiyaye zaman lafiyar su 15 sun ji mummunan rauni. Ping yayi tur da wannan harin.

Har yanzu babu tabbas kan yadda aka kai farmakin. Kungiyar ‘yan tsagera ta al-Shabab ta ce ta tura ‘yan kunar-bakin-wake su biyu cikin sansanin, daya a kafa, dayan kuma cikin mota. Jami’an Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka kuwa, cewa suka yi an kai harin kwanson bam ne a kan sansanin.

Har yanzu ana fama da tashin hankali a Mogadishu, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da ta janyo ‘yan kishin Islama masu sassaucin ra’ayi cikin gwamnati. Kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi kamar al-Shabab sun yi watsi da yarjejeniyar, sun kuma lashi takobin kai hari kan sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka wadanda su ne ke kula da muhimman cibiyoyin gwamnati. Rundunar ta Tarayyar Afirka ta kunshi sojoji dubu 3 daga Uganda da Burundi.

XS
SM
MD
LG