Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 14, Ciki Har Da Sojojin Amurka Hudu, Da Na Britaniya Biyu A Afghanistan


Wasu hare-haren bama-bamai a gabashi da kuma kudancin Afghanistan sun kashe mutane 14 jiya lahadi, cikinsu har da sojojin Amurka hudu da na Britaniya biyu, yayin da sojojin kawance da na Afghanistan suka kashe mutane biyar da ake kyautata zaton 'yan tsagera ne.

Wani kakakin rundunar sojojin dake karkashin NATO a Afghanistan yace bam da aka boye a gefen hanya ya tashi ya kashe sojojin na Amurka a lardin Nangarhar a gabashin kasar.

Ma'aikatar tsaron Britaniya ta ce sojojin Britaniya biyu sun mutu a lokacin tashin bam yayin da suke yin sintiri a gundumar Garmsir ta lardin Helmand a kudancin kasar.

A Kabul, babban birnin kasar, wani dan harin kunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa a kusa da kwambar motocin NATO, amma kuma wasu fararen hula 'yan Afghanistan su biyu ya kashe.

Wani bam din ya tashi a kusa da motar wani magajin gari a birnin Kandahar a kudancin kasar. Magajin garin ya kubuta, amma wani farar hula ya mutu.

A jiya lahadi kuma, rundunar sojojin Amurka ta ce sojojin kawance da na Afghanistan sun kashe 'yan ta kife biyar a lardin Kandahar.

XS
SM
MD
LG